Hebrews 5

1Akan zaɓi kowane babban firist daga cikin mutane ne, akan kuma naɗa shi domin yǎ wakilce su a kan alʼamuran Allah, domin yǎ miƙa kyautai da hadayu saboda zunubai. 2Da yake babban firist ɗin mai kāsawa ne, yana iya bin da jahilai da kuma waɗanda suka kauce hanya, a hankali. 3Shi ya sa dole yǎ miƙa hadayu domin zunubansa, da kuma domin zunuban mutane.

4Ba wanda yakan kai kansa a wannan matsayi mai girma; sai ko Allah ya kira shi, kamar yadda aka yi wa Haruna. 5Haka ma Kiristi bai kai kansa neman ɗaukaka na zama babban firist ba. Allah ne dai ya ce masa,

“Kai Ɗana ne;
yau na zama Uba a gare ka.”
Zab 2.7

6Ya kuma ya ce a wani wuri,

“Kai firist ne na har abada,
bisa ga tsarin Melkizedek.”
Zab 110.4

7A lokacin da Yesu ya yi rayuwa a duniya, ya yi adduʼoʼi da roƙe-roƙe tare da kuka mai zafi da kuma hawaye ga wannan wanda yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa ji shi saboda tsananin bangirman da ya yi. 8Ko da yake shi ɗa ne, ya yi biyayya ta wurin shan wahala 9kuma da aka mai da shi cikakke, sai ya zama hanyar samun madawwamin ceto ga dukan waɗanda suke masa biyayya. 10Allah kuwa ya naɗa shi yǎ zama babban firist, bisa ga tsarin Melkizedek.

Gargaɗi game da Kaucewa

11Muna da abubuwa masu yawa da za mu faɗa game da wannan batu, sai dai yana da wuya a bayyana, da yake ba ku da saurin ganewa. 12Gaskiya, a yanzu ya kamata a ce kun zama malamai, sai ga shi kuna bukatar wani yǎ sāke koya muku abubuwa masu sauƙi game da abin da Allah ya faɗa. Kuna bukatar madara, ba abinci mai ƙauri ba! 13Duk wanda yake rayuwa a kan madara, shi kamar jariri ne har yanzu, kuma bai san ainihi mene ne ya dace ba. 14Amma abinci mai ƙauri na balagaggu ne, waɗanda suka hori kansu don su bambanta tsakanin nagarta da mugunta.

Copyright information for HauSRK